Shugabar Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta ce tsauraran matakan binciken manyan motoci a kan iyakar Rafah da ke tsallakawa daga Masar zuwa Gaza na rage kai kayan agaji.
Cindy McCain ta ce, “Aikin ba na masu hankali bane,” ta kara da cewa duk da cewa ta fahimci cewa ana bukatar bincike don tabbatar da cewa ba a safarar makamai ba, ya kamata a samu saukin shigar da abinci.
Babbarn Darakta na shirin samar da abinci na duniya ta kara da cewa, “Mun samu manyan motoci ‘yan kadan a ciki.”
“Muna buƙatar shigar da adadi mai yawa. Muna buƙatar shiga cikin aminci, ba tare da katsewa ba a cikin Gaza domin mu ciyar da kuma tabbatar da cewa mutane ba su kwana da yunwa ba, saboda abin da ke faruwa ke nan.”
A lokacin da ya ziyarci Masar domin ganawa da jami’ai, McCain ya ce kowace babbar mota ta sauke kayan ta a wani shingen bincike domin dubawa, sannan a sake dora ta idan an kammala .
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply