Iyalan masarautar Malaysia sun zabi Sultan Ibrahim Sultan Iskandar mai iko kuma mai fada a ji daga jihar Johor a kudancin kasar domin ya zama sarkin kasar.
Sarkin dai na taka rawar gani sosai a kasar Malesiya, amma masarautar ta kara yin tasiri a ‘yan shekarun nan saboda rashin zaman lafiya da aka dade a siyasance wanda ya sa sarki mai ci ya yi amfani da karfin ikon da ba kasafai ake amfani da shi ba.
Malesiya tana da wani tsari na musamman wanda Shuwagabannin iyalai tara na Sarautarta ke yin sarauta na tsawon shekaru biyar.
Kasar Kudu maso Gabashin Asiya dimokuradiyya ce ta majalisar dokoki, tare da sarki ya zama shugaban kasa.
Sultan Ibrahim zai karbi mulki daga hannun Sarki Al-Sultan Abdullah a ranar 31 ga watan Junairu, 2024, in ji mai kare hakin sarakunan a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.
Ba kamar sauran sarakunan gargajiya na Malaysia ba, Sultan Ibrahim ya kasance mai fafutuka kan harkokin siyasa kuma ya ce yana da kyakkyawar alaka da Firayim Minista Anwar Ibrahim.
Sarkin wanda aka san yana da tarin manyan motoci na alfarma da babura, yana da sha’awar kasuwanci iri-iri tun daga kadarori zuwa ma’adinai.
Sarki Al-Sultan ya taka rawar gani da ba a saba gani ba a siyasar Malaysia, inda ya zabi firaministan kasar uku na karshe.
Kundin tsarin mulkin tarayya ya bai wa sarki wasu ‘yan madafun iko, inda ake bukatar sarki ya yi aiki da shawarar Firayim Minista da majalisar ministoci.
Har ila yau, ya bai wa sarkin damar nada Firayim Minista wanda ya yi imanin yana da rinjayen majalisa, ikon da ba a taba amfani da shi ba har sai 2020, kamar yadda aka saba zabar Firimiya ta hanyar zabe.
REUTERS/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply