Hukumar Jin dadi alhazan jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta bayyana naira miliyan hudu da dubu dari biyar a matsayin kudin ajiya na aikin hajjin bana kafin samun cikkaken bayani daga hukumar alhazai ta kasa.
Shugaban hukumar Alhaji Mohammed Awwal Aliyu shine ya bayana hakan a lokacin da ya kaddamar da fara karbar kudaden aikin hajjin bana a offishin hukumar dake Minna.
Alhaji Mohammed Awwal Aliyu ya ce “hukumar ta kaddamar da fara karbar kudaden ne da nufin fara ayyukan ta cikin sauri domin kaucewa duk wasu matsaloli da ka iya kawo cikas ga ayyukan ta yayin aikin hajjin bana.”
Awwal Aliyu ya Kara da cewar yanzun haka an tsara karbar naira miliyan hudu da dubu Dari biyar ne a matsayin kudin aikin hajjin kafin samun cikkaken bayani daga hukumar alhazai ta kasa NAHCON.
Ya ce “hukumar ta kammala shirin ta na ganin ta fara gudanar da aikin cikin sauri , da kuma tsara yadda aikin zai tafi kamar yadda aka tsara.”
Shugaban hukumar ya Kuma gargadi ma’aikatan hukumar musamman APOs dake kananana hukumomi 25:dake fadin jihar da su bi dukkanin tsare tsaren da dokokin da aka shinfida, kana ya ce Kara su sayar da form da hukumar ta fitar ga maniyata.
Har ila yau Awwal Aliyu ya bukaci su da Kar karbi kudin maniyata Kai tsaye, akwai hanyoyin da aka tsara na biyan kudaden ta hanyar bankuna, kana ya ce su guji karbar na goro yayin gudanar da ayyukan su, inda ya ce hukumar bazata zura Ido Hakan na faruwa ba.
Shugaban ya Kuma bayana cewar a bana hukumar aikin hajji ta kasa ta warewa jihar Neja kujeru 3,592, inda ya ce hukumar Jin dadi alhazai jihar ta Kamala tsara raba kujerun ga kananana hukumomi jihar 25 .
A jawabin sa a Taron Shugaban kwamitin kula da harkokin adinin na majalisar dokokin jihar Neja Abdullahi Isah ya baiwa hukumar tabbacin majalisar na ganin ta bata gagarumin hadin Kai domin ganin ta sami nasarar tafiyar da ayyukan ta kamar yadda ta tsara
Ya Kuma shawarci ma’aikatan da su rike gaskiya da Amma yayin gudanar da ayyukan su.
Haka shima a jawabin sa APOsbna karamar hukumar Chanchaga kana Shugaban majalisar APos na Kannan hukumomi 25 Alhaji Abu Sufyan Ahamad Sirisiri ya yaba da yadda aka fara aikin cikin sauri kana ya bukaci hukumar da ta taimaka wajan samar masu da karin kudade domin ganin sun gudanar da ayyukan su cikin sauki.
Taron Wanda ya hada dukkanin manyan ma’aikatan hukumar, a karshe an mikawa APOs kaso na kujerun da aka warewa kowace karamar hukuma.
Nura Muhammed.
Leave a Reply