Tsohon firaministan kasar Sin Li Keqiang ya mutu sakamakon bugun zuciya yana da shekaru 68 a ranar Juma’a, watanni kadan bayan ya yi murabus daga mukaminsa na shekaru goma.
Masanin tattalin arziki, ya goyi bayan bunƙasa tattalin arziƙin kasuwa, yana ba da shawarar yin gyare-gyare a bangaren samar da kayayyaki ta hanyar da aka yiwa lakabi da “Likonomics” wanda ba a taɓa aiwatar da shi sosai ba.
“Comrade Li Keqiang, yayin da yake hutawa a birnin Shanghai a cikin ‘yan kwanakin nan, ya fuskanci bugun zuciya ba zato ba tsammani a ranar 26 ga Oktoba, kuma bayan duk kokarin da aka yi na farfado da shi ya ci tura, ya mutu a Shanghai da mintuna goma da tsakar daren ranar 27 ga watan Oktoba,” in ji gidan talabijin na CCTV na kasar.
Li ya kasance firayim minista kuma shugaban majalisar ministocin kasar Sin a karkashin Xi na tsawon shekaru goma har ya sauka daga dukkan mukaman siyasa a watan Maris.
REUTERS/Ladan Nasidi.
Leave a Reply