Take a fresh look at your lifestyle.

SHUGABAN SOJIN BURKINA FASO YA KORI MINISTAN

0 120

Shugaban mulkin sojan Burkina Faso, Kanar Paul-Henri Damiba, ya kori ministan tsaronsa.

 

A cikin wasu hukunce-hukunce guda biyu da aka karanta a gidan talabijin na kasar, shugaban mulkin sojan ya ce ya kori Janar Barthelemy Simpore tare da daukar nauyin da kansa.

 

Sanarwar ba ta bayar da dalilan da suka sa aka yi wa majalisar ministocin garambawul ba.

 

Kanar Damiba ya karbe mulki a watan Janairun da ya gabata, yana mai zargin gwamnatin da ta gabata da gazawa wajen magance matsalolin da ke addabar yankin yammacin Afirka, ciki har da ‘yan tawaye masu kishin Islama.

 

Dubban mutane ne aka kashe a rikicin sannan kuma mutane kusan miliyan biyu suka rasa matsugunansu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.