Take a fresh look at your lifestyle.

Hare-haren Da Isra’ila Ke Kaiwa Kan Gaza Na Haifar Da Bala’i Zai Iya Daukar Shekaru Goma-Lavrov

0 285

Ministan harkokin wajen Rasha ya ce harin bam da Isra’ila ke kaiwa Gaza na da hatsarin haifar da bala’in da ka iya daukar shekaru da dama.

 

Sergey Lavrov ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Belta na kasar Belarus, inda ya ce ba zai yuwu a rusa Hamas ba kamar yadda Isra’ila ta yi alkawarin yi ba tare da lalata Gaza ba, tare da yawancin fararen hula.

 

“Idan aka lalata Gaza kuma aka kori mutane miliyan biyu, kamar yadda wasu ‘yan siyasa a Isra’ila da ketare suka ba da shawara, wannan zai haifar da bala’i na shekaru da yawa,” in ji Lavrov.

 

 

 

ALJAZEERA/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *