Kakakin ma’aikatar lafiya ta Gaza, Ashraf al-Qudra ya yi jawabi ga manema labarai bayan bayar da karin adadin wadanda suka mutu a baya da muka ruwaito a baya.
Ya ce kazamin harin bama-bamai da Isra’ila ta kai ya mayar da Gaza zuwa “kwallon wuta”, inda a kalla Falasdinawa 377 suka rasa rayukansu a wuraren da aka kebe.
Al-Qudra ya kara da cewa matakin na Isra’ila ya haifar da gurgunta tsarin kiwon lafiya, da kungiyoyin likitoci da motocin daukar marasa lafiya a Gaza.
Da yake maimaita kiran neman taimakon kasashen duniya, ya kuma yi kira ga daliban likitanci da ma’aikatan jinya da suka yi ritaya da su fito.
Hukumomin lafiya a Gaza sun ce a ranar Juma’a an kashe Falasdinawa 7,326 tun lokacin da Isra’ila ta fara kai hare-hare.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply