Take a fresh look at your lifestyle.

Koriya Ta Arewa Ta Tabbatar Da Rufe Ofisoshin Jakadancin Ta Da Dama

0 103

Koriya ta Arewa ta tabbatar a ranar Juma’a cewa ta rufe wasu ofisoshin jakadancinta a kokarinta na “sake daidaita karfin diflomasiyyar ta yadda ya kamata.”

 

Koriya ta Arewa na shirin rufe kusan ofisoshin jakadancin ta guda goma da suka hada da na Spain, Hong Kong, da kasashe daban-daban na Afirka, a cewar rahotannin kafafen yada labarai da manazarta, wanda hakan na iya nufin rufe kusan kashi 25% na ayyukanta a duniya.

 

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ya tabbatar a cikin sharhin da aka yi a shafin yanar gizon ma’aikatar cewa an rufe wasu ayyuka yayin da ya kara da cewa an bude wasu sabbi.

 

Kakakin ya ce, “Muna gudanar da ayyukan janyewa da kafa ofisoshin diflomasiyya daidai da sauyin yanayi na duniya da manufofin ketare na kasa,” in ji Kakakin, yana mai kira da aiki na yau da kullun, ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

 

 

 

REUTERS/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *