Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da cewa Dakarun ta sun yi wa babban birnin Gaza kawanya yayin da suka yi watsi da kiraye-kirayen da kasashen duniya ke ci gaba da yi na tsagaita bude wuta domin dakatar da zubar da jini a yankin Falasdinawa.
Kakakin rundunar sojin Isra’ila Daniel Hagari ya ce an kewaye birnin Gaza kusan mako guda bayan Dakarun ta sun fadada ayyukan su na kasa a yankin da ke karkashin ikon Hamas.
Hagari ya ce “A halin yanzu kwata-kwata ba a kan teburin sulhu “.
Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda a makon da ya gabata ya ce yakin da ake yi da Hamas ya shiga “mataki na biyu” a cikin yakin kasa da ke kara ta’azzara, ya fada a daren ranar Alhamis cewa Sojojin Isra’ila suna kan “mafi girman yakin”.
Bangaren sojan Hamas, Qassam Brigades, ya yi gargadi a mayar da martani cewa Gaza za ta zama “la’anar tarihi ga Isra’ila” kuma sojojin Isra’ila da ke shiga yankin gawarwakin su za su koma gida “cikin bakar jaka”.
A jiya alhamis, masu aiko da rahotanni na musamman na Majalisar Dinkin Duniya 7 sun fitar da wata sanarwa da suka yi kira da a tsagaita bude wuta a Gaza, inda suka bayyana damuwarsu kan cewa Falasdinawa na fuskantar babban hadarin kisan kiyashi.
Hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza na fuskantar karin tofin Allah tsine tun bayan da dakarunta suka kai farmaki ta sama a jere a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza.
Akalla mutane 195 ne suka mutu yayin da wasu daruruwa suka jikkata a hare-haren da aka kai a ranakun Talata da Laraba, a cewar Jami’ai a yankin da ke karkashin ikon Hamas.
Akalla Falasdinawa 9,061 aka kashe a harin bam da aka kai a Gaza, wanda sojojin Isra’ila suka kaddamar a matsayin martani ga Hamas na ranar 7 ga Oktoba.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply