Take a fresh look at your lifestyle.

LABARI: Rundunar Sojoji Da ‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Wasu Masu Yima Kasa Hisima Su 2 A Jihar Katsina

0 192

Dakarun Sojojin Najeriya na Bataliya ta 17 tare da hadin gwiwar ‘yan sanda sun ceto wasu masu yima kasa hidima biyu da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a unguwar Yargoje da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.

 

KU KARANTA KUMA: Jihar Kano: Sojoji da DSS sun kama wasu mutane 2 da ake zargin ‘yan ta’adda ne

 

Wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta bayyana cewa, kokarin da jami’an tsaro suka yi ne ya sa aka kwato wadanda aka sace tare da dawo da su lafiya a wani farmakin hadin gwiwa da suka kai ranar Alhamis 2 ga watan Nuwamba 2023.

 

Daraktan ya kara da cewa, daukin gaggawa da ceto da hadin gwiwar sojojin Birgediya 17 da ‘yan sandan Najeriya suka nuna ya yi nasarar ceto wadanda lamarin ya rutsa da su daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

 

“An ba wa ‘yan kungiyar da aka ceto kulawar da suka dace da kuma tallafa musu domin tabbatar da lafiyar jikinsu da kuma tunanin su kuma a halin yanzu suna hannun ‘yan sandan Najeriya da ke Kankara.

 

“Rundunar Sojin Najeriya na ci gaba da neman hadin kai da goyon bayan jama’a wajen samar da bayanan da suka dace don inganta ayyukan sojojin da suke yi na tunkarar masu aikata laifuka da ke barazana ga tsaron kasar.”

 

Idan dai za a iya tunawa, an yi garkuwa da masu hima kasa hidima ne a lokacin da suke kan hanyarsu daga jihar Edo zuwa jihar Katsina.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *