Shugaban kasar Chile Gabriel Boric wanda ya yi Allah wadai da harin bama-bamai ta sama da sojojin Isra’ila suka kai a zirin Gaza, ya sanya Janye Jakadan shi daga Isra’ila, ya shaidawa shugaban Amurka Joe Biden cewa abin da Isra’ila ta yi ya saba wa dokokin kasa da kasa.
“Wadannan hare-haren Israilas ba tare da hujja ba sun cancanci la’antar duniya. Amma martanin da gwamnatin Benjamin Netanyahu ya bayar kuma ya cancanci a hukunta su,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Boric yana cewa bayan ganawa da Biden a fadar White House.
“Babu shakka za mu iya cewa martanin bai dace ba kuma yana keta dokar jin kai ta kasa da kasa,” in ji shi.
“Hakkin wata kasa na kare kanta yana da iyaka, kuma iyakokin suna nuna mutunta rayukan fararen hula marasa laifi, musamman yara, da mutunta dokokin jin kai.”
Da aka tambaye shi game da martanin da Biden ya bayar, Boric ya ce ba hurumin shi bane ya yi magana da Shugaban Amurka.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply