Take a fresh look at your lifestyle.

TSOHON SHUGABAN PDP NA JIHAR YOBE, TATA YA YI MURABUS DAGA JAM’IYYAR

0 90

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP, kuma dan takarar gwamna a jihar Yobe, Abba Gana Tata, ya fice daga jam’iyyar.

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Tata da aka aika zuwa Massaba Ward na jam’iyyar PDP a jihar.

 

Wani bangare na wasikar ya kara da cewa, “Wannan shine don sanar da ku cewa na fice daga jam’iyyar PDP daga ranar Talata 13 ga watan Satumba 2022.

 

“A haɗe da wannan katin zama memba mai lamba 1533599.

 

“Yayinda na gode muku da jam’iyya, ku karbi fatan alheri na”.

 

Abba Gana Tata bai bayyana dalilan ficewa daga jam’iyyar ba karara.

 

An kuma aika kwafin takardar murabus din ga shugaban karamar hukumar Bursari da kuma shugaban jam’iyyar na jiha.

 

 

 

 

 

DailyPost/N.O

Leave A Reply

Your email address will not be published.