Take a fresh look at your lifestyle.

Gaza: Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce An Lalata Wuraren Samar Da Ruwa Bakwai

0 121

Hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa, wuraren ruwa guda bakwai a zirin Gaza sun “kaitse tare da babbar barna” a ranakun Asabar da Lahadi.

 

A cewar sabon sabuntawar UNOCHA, rijiyoyin ruwa guda biyu a Rafah, bututun najasa guda uku a cikin garin Gaza da tafkunan ruwa guda biyu duk sun lalace.

 

Mahukuntan Gaza ta yi gargadi kan hadarin da ke tattare da ambaliya na najasa.

 

A ranar Asabar din da ta gabata ne wani faifan bidiyo ya nuna yadda ruwa ke gudu a kan titi bayan da wata tankar ruwa da ke Tal Al Zaatar da ke arewacin Gaza ta lalace.

 

 

 

ALJAZEERA/Ladan Nasidi.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *