Ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar da cewa, an kai wani samame ta sama a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Maghazi da ke tsakiyar Gaza cikin dare, inda aka kashe mutane 40 tare da jikkata wasu 34 na daban.
Arafat Abu Mashaia, wanda ke zaune a sansanin, ya ce hare-haren ta sama sun rugza wasu gine-ginen gidaje masu yawan gaske, inda mutanen da aka tilastawa barin wasu yankunan Gaza suke mafaka.
“Kisan kiyashi ne na gaske,” in ji shi, yana tsaye a kan tarkacen. “Duk a nan mutane ne masu zaman lafiya. Ina kalubalantar duk wanda ya ce akwai juriya [mayaka] a nan.”
Sansanin, wani katafaren wurin zama, yana cikin yankin da sojojin Isra’ila suka bukaci Falasdinawa farar hula da su nemi mafaka a yayin da suke mayar da hankali kan hare-haren da sojojin suka kai a Arewa.
Jiragen yakin Isra’ila sun kuma kai hari kan sansanonin ‘yan gudun hijira guda biyu a zirin Gaza, inda suka kashe akalla mutane 53 tare da jikkata wasu da dama, a cewar jami’an lafiya a yankin da aka yi wa kawanya.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply