Fadada yakin da ake yi a Gaza “ba makawa” ne saboda karuwar ta’addancin Isra’ila, a cewar ministan harkokin wajen Iran.
Hossein Amirabdollahian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani, kamar yadda tashar talabijin ta Press TV ta Iran ta ruwaito a ranar Juma’a.
“Saboda fadada tsananin yakin da ake yi da fararen hula mazauna Gaza, fadada iyakokin yakin ya zama babu makawa,” in ji Amirabdollahian.
Ba a san abin da yake nufi da “faɗan da ba makawa” na rikicin.
Na dabam, Amir Abdollahi ya fada a cikin shafin shi na X ranar Alhamis: “Lokaci yana kurewa da sauri don ci gaba da laifukan Tel Aviv.”
Ya kara da cewa, “Amfanin Netanyahu kawai shi ne yadda ya sanya tushe na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya kara girgiza tare da nuna masu laifi, masu tayar da hankali, da kuma ta’addancin gwamnatin sahyoniyawa a kisan gillar da aka yi wa mata da kananan yara a Gaza.”
“Ba shakka, makomar ta Falasdinu ce,” Amir Abdollahi ya rubuta.
Rikicin yanki da rikicin kan iyaka ya kara tsananta tun bayan da kungiyar Hamas mai samun goyon bayan Iran da ke jagorantar yankin Gaza ta kai hari kan Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, lamarin da ya janyo yakin Isra’ila a yankin.
Isra’ila da kungiyar Hezbollah ta Lebanon, da ke kawance da Hamas, sun musanya hare-hare. Sama da mayakan Hizbullah 60 da fararen hula 10 ne aka kashe a cewar jami’an tsaron kasar Lebanon.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply