Take a fresh look at your lifestyle.

Zaben Jihar Kogi: ‘Yan Sanda Sun Hana Jami’an Tsaro Raka VIP Zuwa Rumfunan Zabe

0 80

Yayin da ake gudanar da zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba a yau a jihohi uku daban-daban (Bayelsa, Imo, da Kogi) na kasar nan, mataimakin sufeto-janar na ‘yan sandan da aka tura domin sa ido kan zaben gwamnan jihar Kogi, Mista Habu Sani, ya ce ya haramta wa jami’an tsaro raka VIPs zuwa rumfunan zabe.

 

Hakan ya fito ne ta wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Sufeto Williams Ovye-Aya, ya fitar a Lokoja, babban birnin jihar.

 

“Babu wani dalili da ya kamata a bar duk wani jami’in tsaro da ke da alaka da VIPs, jami’an siyasa da na jama’a ko kuma wani mutum a fadin jihar ya yi motsi ko raka shugabannin su a lokacin hana zirga-zirgar ababen hawa.

 

“Duk wani jami’in da aka kama yana karya wannan odar ta hanyar rakiyar duk wani jami’in VIP, jami’an siyasa da na jama’a ko kuma wani mutum zuwa rumfar zabe, za a kama shi kuma a hukumta shi.

 

“Saboda haka, manyan jami’an VIP, ‘yan siyasa da na jama’a da za su kada kuri’a su lura da wannan Dokar saboda gujewa duk wani abin kunya da zai same su.

 

“Wannan saboda ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ba za su bari a tauye duk wani abu na tsaro a lokacin zaben ba,” in ji shi.

 

 

 

NAN/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *