Take a fresh look at your lifestyle.

Bana Goyon Bayan Ikiarin Israila Na Kubutar Da Falasdinawa Daga Hannun Hamas-Jakada

0 99

Jakadan Falasdinawa a Najeriya Abdallah Abu Shawesh, ya nuna rashin amincewa da ikirari da gwamnatin Isra’ila ta yi na cewa tana kokarin kare Falasdinawa da kubutar da Falasdinawa daga hannun kungiyar Hamas.

 

Jakadan Falasdinawa, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin Najeriya.

 

Ya bayyana cewa, kasar shi ba ta karkashin kungiyar Hamas ta yi garkuwa da ita, yana mai cewa gaba daya ra’ayin na daga hankali ne.

 

“Ba mu kasance karkashin garkuwar Hamas ba, uzuri ne na Isra’ila don tabbatar da mamayar su. Shin don ku ‘yanta ni ne ku kashe ni? Idan wannan hanya ce ta taimaka wa Falasdinawa, ba za mu iya yarda da shi ba.

 

Falasdinawa ba su taba neman taimakon Isra’ila don kwato su daga Hamas ba. Hamas, kamar sauran kungiyoyi a Falasdinu, suna adawa da mamayar Isra’ila, Hamas ba ta taba kai hari ga wata kasa ba. An kirkiro Hamas shekaru 20 bayan mamayar Isra’ila, “in ji shi.

 

Ambasada Shawesh, ya yi nuni da cewa, hare-haren bama-bamai da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa a zirin Gaza, ya hana daukacin al’ummar kasar biya wa kan su duk wata bukata.

 

“Mataki ne mai matukar hatsari, inda muka saba da kirga adadin wadanda suka mutu, barnar gidaje, raunuka, da sauransu da ba tare da wani jin dadi ga wadanda abin ya shafa ba.”

 

Ya bayyana cewa a cewar Majalisar Dinkin Duniya, kashi 70% na Falasdinawa a halin yanzu suna gudun hijira.

 

Ya kara da cewa “Duk wadannan ba adadi ba ne kawai, mafarkai ne, bege da buri.”

 

Sama da Falasdinawa 11,000 ne aka kashe a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan, tare da jikkata sama da mutane 29,500 tun daga ranar 7 ga Oktoba.

 

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinawa a zirin Gaza ta tabbatar da adadin mutanen da suka mutu, inda ta ce adadin ya hada da akalla yara 4,500.

 

Ma’aikatar ta ce adadin wadanda suka mutu ya haura a kalla 11,200 a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye, tare da jikkata sama da mutane 29,500.

 

Wakilin Falasdinawa, ya yi shakkun yuwuwar kawar da kungiyar Hamas a lokacin da ake ci gaba da mamayar kasarsu.

 

Ya ce “abin da Hamas ke yi wani tunani ne da ya sa ba zai yiwu a kashe shi ba. Ba zai yiwu a kashe ra’ayi ba. Ba zai yi aiki ba. Hanyoyin siyasa ne kawai za su iya magance matsalar .

 

A halin da ake ciki gwamnatin Isra’ila ta yi zargin cewa Hamas na amfani da asibitoci, da wuraren kiwon lafiya da wuraren wasanni a matsayin garkuwa.

 

Jakadan kasar Isra’ila a Najeriya, Michael Freeman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ofishin jakadanci a Najeriya ya fitar

 

“Hamas na cin mutuncin Falasdinawa na Gaza a matsayin garkuwa,” in ji shi.

 

Sai dai Hamas ta musanta ikirarin sojojin Isra’ila na amfani da fararen hula da asibitoci a matsayin garkuwa.

 

A wani labarin kuma kakakin rundunar tsaron Isra’ila Rear Admirar Daniel Hagari ya ce kungiyar Hamas na da wasu gine-gine na karkashin kasa karkashin asibitin Shifa da ke zirin Gaza wadanda shugabannin su ke amfani da su wajen kai hare-hare kan Isra’ila.

 

Kakakin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya fada jiya Juma’a cewa al-Shifa na fuskantar hare-haren bama-bamai, inda ya kara da cewa asibitoci 20 a zirin Gaza ba su aiki.

 

Da aka tambaye ta game da yuwuwar harin da Isra’ila ta kai kan asibitin al-Shifa a ranar Juma’a, mai magana da yawun hukumar ta WHO Margaret Harris ta ce a cikin wani takaitaccen bayani: “Ban samu cikakken bayani kan al-Shifa ba amma mun san ana kai musu hare-hare da ruwan bama -bamai.”

 

Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin da yammacin jiya Juma’a cewa wani makami mai linzami da aka harba daga cikin Gaza ne ya haddasa harin da aka kai a asibitin al-Shifa.

 

Sama da wata guda kenan da Hamas ta kai wa Isra’ila hari tare da ayyana yakin ta da Hamas.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *