Sojojin Isra’ila sun kai hari a kofar gaban asibitin al-Shifa na birnin Gaza, inda dubban marasa lafiya da Falasdinawan da suka rasa matsugunansu ke samun mafaka.
Shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ya shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa ana kai wa asibitocin Gaza hari da gangan don tilasta wa fararen hula ficewa daga Gaza.
Isra’ila ta ce Falasdinawa 100,000 ne suka koma kudu a Gaza a cikin kwanaki biyun da suka gabata, sai dai Falasdinawa da dama sun ce suna cikin tarko yayin da ake ci gaba da gwabza fada.
Akalla Falasdinawa 11,078 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply