Take a fresh look at your lifestyle.

‘Muna Dab Da Mutuwa Cikin ‘Yan Mintuna’: Shugaban Asibitin Gaza

0 274

Daraktan Asibitin Gaza Al-Shifa ya fada wa Al Jazeera cewa rukunin magunguna da likitoci “sun yanke gaba daya, duk wani mai rai da sojojin Israila suka gani yana tafiya sais u kai mashi hari”.

 

Shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ya shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa ana kai wa asibitocin Gaza hari da gangan don tilasta wa fararen hula ficewa daga Gaza.

 

Isra’ila ta ce Falasdinawa 100,000 ne suka koma kudu a Gaza cikin kwanaki biyun da suka gabata; Falasdinawa da dama sun ce har yanzu suna cikin tarko yayin da ake ci gaba da gwabza fada.

 

Akalla Falasdinawa 11,078 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba. A Isra’ila, bayan wani bita da aka yi a baya, ta ce adadin wadanda suka mutu ya haura 1,200.

 

 

ALJAZEERA/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *