Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana ambaliya da ta raba dubban daruruwan mutane a Somaliya da makwaftan kasashen gabashin Afirka a matsayin wani abu da aka taba yi a cikin karni.
Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce sama da mutane miliyan 1.5 ne za su iya shafan mamakon ruwan sama mai karfin gaske a Somaliya, wanda ya kara dagulewa sakamakon hadewar al’amuran yanayi guda biyu – illar El Niño da na Dipole na Tekun Indiya.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya fara a farkon watan Oktoba ya biyo bayan matsanancin fari da aka shafe watanni ana yi a yankin.
Fiye da mutane 300,000 ne aka tilastawa barin gidajensu a Somaliya kuma an mamaye garuruwa da kauyuka a fadin arewacin Kenya.
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply