An fara tantancewa da kidayar kuri’u a rumfunan zabe da dama a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.
A yankin Zamara-Okordia da ke babban birnin jihar, an ga jami’an hukumar zabe mai zaman kanta suna kidayar kuri’u a bainar jama’a wadanda suka kada kuri’a.
A unguwa 4, sashi na 5 na karamar hukumar, masu kada kuri’a na ci gaba da kada kuri’a har ma lokacin zabe ya kare.
Ana kuma ci gaba da kidayar kuri’u a Sampou, karamar hukumar Kolokuma-Opokuma, mahaifar Gwamna mai ci Duoye Diri.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply