Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Usman Ododo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a ranar Asabar.
Jami’in zaben jihar, Farfesa Johnson Urama wanda kuma shi ne mataimakin shugaban jami’ar Najeriya Nsuka, jihar Enugu, ya sanar da sakamakon zaben da yammacin ranar Lahadi a cibiyar tattara sakamakon zaben jihar da ke Lokoja, babban birnin jihar.
Ya ce Ododo na APC ya samu kuri’u 446,237 inda ya lashe zaben daga cikin jimillar kuri’u 791, 890 da aka kada a zaben.
“Bayan tantance adadin kuri’un da ake bukata da kuma ikon da ya shafe ni a matsayina na babban jami’in zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, ni Farfesa Johnson Uramahi, na bayyana Usman Ododo a matsayin dan takarar jam’iyyar All Progressives. Congress, APC, a matsayin wanda ya yi nasara kuma an dawo da shi kamar yadda aka zaba,” inji shi.
Dan takarar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Murtala Ajaka ya zo na biyu da kuri’u 259,052 yayin da Dino Melaye na jam’iyyar PDP ya zo na uku da kuri’u 46,362.
Adadin wadanda suka yi rajista a zaben ya kai 1,932,474, yayin da adadin wadanda aka amince da su ya kai 794,500.
Jimlar kuri’u masu inganci sun kai 782,289, yayin da adadin kuri’un da aka ki amincewa ya kai 9,601.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply