Firayim Ministan Burtaniya Rishi Sunak ya kori ministar harkokin cikin gida Suella Braverman, daya daga cikin manyan Ministocinsa, wata majiya ta gwamnati ta bayyana a ranar Litinin, biyo bayan kalaman da ta yi a makon da ya gabata game da yadda ‘yan sanda ke tafiyar da wani tattaki na goyon bayan Falasdinu.
A makon da ya gabata Braverman ya bijirewa Sunak ta hanyar buga labarin da ya kai hari kan yadda ‘yan sanda ke tafiyar da tattakin da ya gudana a ranar Asabar.
Masu sukar sun ce matakin nata ya taimaka wajen ruruta wutar rikici tare da karfafa masu zanga-zangar dama su fito kan titunan birnin Landan, lamarin da ya sanya Sunak cikin matsin lamba kan daukar mataki.
REUTERS/Ladan Nasidi.
Leave a Reply