Kamfanin dillancin labaran kasar ORTM ya habarto cewa, sojojin kasar Mali sun kwace iko da garin Kidal da ke arewacin kasar, wanda ke zama karo na farko da sojojin kasar ke rike da tungar ‘yan tawayen Abzinawa cikin kusan shekaru goma.
“Wannan sako ne daga shugaban rikon kwarya zuwa al’ummar Mali,” in ji dan jarida Ibrahim Traore a cikin gabatarwar shi ga jaridar ORTM. “A yau jami’an mu dauke da makamai da jami’an tsaro sun kwace Kidal. Aikin mu bai kare ba”.
Mohamed Maouloud Ramadan, kakakin ‘yan tawayen dake makwabciyarta Mauritania, ya tabbatar da kasancewar sojojin Mali a Kidal.
Sojojin kasar Mali tare da wasu takwarorinsu na dan kwangilar sojan kasar Rasha Wagner, sun shafe kwanaki suna fafatawa da mayakan Abzinawa a kokarin da suke yi na kwace garin bayan ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya makonni biyu da suka gabata.
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar ya sanar da ra’ayoyin kasa da kasa cewa #FAMa sun fara aiki a garin #Kidal, 14 ga watan Nuwamba, 2023.
‘Yan tawayen Abzinawa ‘yan aware a arewacin kasar sun dade suna neman kasa mai cin gashin kanta da suka kira Azawad.
A shekara ta 2012, sun kori sojojin Mali daga garin, lamarin da ya haifar da wasu abubuwa da suka dagula al’amura a kasar.
Sojoji masu tayar da kayar baya, sun nuna bacin ransu game da yadda aka tafiyar da tawayen Abzinawa a shekarar 2012, daga bisani suka hambarar da zababben shugaban kasar ta hanyar dimokuradiyya.
A cikin rudanin, nan da nan masu tsattsauran ra’ayi sun kwace iko da manyan garuruwan arewacin kasar da suka hada da Kidal, inda suka sanya tsauraran fassarar shari’ar Musulunci da aka fi sani da Shariah.
A shekara ta 2013 ne Faransa ta jagoranci shiga tsakani na soji domin kawar da masu tsattsauran ra’ayi daga kan karagar mulki, amma daga baya suka sake haduwa suka kwashe shekaru goma suna kai hare-hare kan sojojin Mali da dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD.
Wani juyin mulkin soja a shekarar 2020, karkashin jagorancin shugaban rikon kwarya Colene Assimi Goïta, ya haifar da tabarbarewar dangantaka da abokan huldar kasa da kasa na Mali.
Ministan harkokin wajen Mali ya umarci tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da aka fi sani da MINUSMA ta tashi, kuma sojojin sun bar Kidal a farkon watan Nuwamba.
Africanews/Ladan Nasidi.
Leave a Reply