Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Neja Ya Taya Gwamna Uzodinma Da Sauransu Akan Nasarar Zabe

0 178

Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja ta arewa ta tsakiyar Najeriya ya taya gwamnan jihar Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin ci gaba Hope Uzodinma murnar sake zabensa.

 

A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Bologi Ibrahim ya fitar, Gwamna Umaru Bago ya bayyana nasarar da aka samu a matsayin abin da ya dace. Ya jaddada cewa sake zaben Gwamna Uzodinma ya tabbatar da kyakkyawan tasirin da aka samu a wa’adinsa na farko.

 

Gwamna Bago ya bukaci takwaransa na jihar Imo da ya rubanya nasarorin da ya samu a cikin shekaru hudu masu zuwa, tare da barin abubuwan da ba a taba ganin irinsa ba a jihar. Ya kuma kara karfafa gwiwar Gwamna Uzodinma da ya yi fice wajen samun nasara, tare da mika hannun zumunci ga duk wadanda suka yi takara tare da shi domin amfanin jihar baki daya.

 

Gwamna Umaru Bago ya mika sakon taya murna ga Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa da zababben gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo kan nasarar da suka samu a zaben.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *