Take a fresh look at your lifestyle.

Shirin Samar Da Ruwan Sha Da Tsabtar Muhalli Na SURWASH Ya Samu Nasarori A Jihar Katsina

Kamilu Lawal,Katsina.

0 194

Mahalarta taron karama muna sani akan shirin samar da ruwan sha da tsabtar muhalli mai dorewa wato “SURWASH”daga jihohin dake aiwatar da shirin na arewacin Najeriya sun yaba da irin nasarorin da shirin ya samu wajen tabbatar da samar da ruwan sha da tsabtar muhalli mai dorewa a jihar Katsina

 

 

A taron na kwana biyar wanda ya gudana a jihar Katsina domin yin duba akan nasarar da shirin ya samu a jihohin dake cin gajiyar shirin, yana kuma da nufin cigaban da bin matakai masu mahimmanci domin tabbatar da dorewar shi cikin nasara.

 

 

Jami’in shirin a jihar Katsina, engr. Aminu Dayyabu Safana yace “SURWASH” shiri ne da yake samun tallafin bankin duniya hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da jihohi domin tabbatar da samar da ruwan sha da tsabtar muhalli mai dorewa a cikin al’umma wanda aka kaddamar a shekarar 2021

 

 

Yace jihohin da suka halarci taron a jihar sun kunshi jihohin Kaduna da Gombe da Plateau da jihar ta Katsina mai masaukin baki

 

Aminu Safana ya kara da cewa; “hukumomin dake aiwatar da shirin na SURWASH a jihar Katsina, sun hada da Hukumar samar da ruwan sha a manyan birane (Water Board) da hukumar samar da ruwan sha da tsabtar muhalli a yankunan karkara (RUWASSA) da Kuma hukumar kula da tsabtar muhalli, wato SEPA a takaice wadanda suke aiki kafada da kafada domin aiwatar da shirin cikin nasara.

 

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban hukumar samar da ruwan sha da tsabtar muhalli a yankunan karkara ta jihar Katsina (RUWASSA), Abubakar Suleiman Abukur, ya bayyana cewa a kalkashin shirin na “SURWASH” hukumar ta gina fanfunan tuka tuka sama da dari a yankunan da ake aiwatar da shirin a jihar.

 

“Mun yi ayyuka 145 a yankunan dake amfana da wannan shiri anan jihar, daga cikin su mun zabo al’ummomi guda 120 wadanda suka amfana da fanfunan tuka tuka inda kuma a wasu makarantu da asibitoci muka samar da rijiyoyi masu amfani da hasken rana da kuma matsugunai na bahaya domin magance matsalar magewayi a wuraren”, inji Abukur.

 

Shima da yake nasa jawabin a wajen taron shugaban hukumar samar da ruwan sha a birane (Water Board) ta jihar Katsina, engr. Tukur Hassan Tingilin yace hukumar ta samar da tashoshi da tankunan ruwa hadi da shimfida hanyoyin daukar ruwa wato pipe pipe domin daukar ruwan su isa ga unguwannin da ake bukata.

 

Tingilin ya kara da cewa;“mun samar da na’urar wuta mai amfani da hasken rana a wasu cibiyoyin samar da ruwan domin dorewar aikin halba ruwan zuwa ga al’umma”.

 

A cikin kwanakin da taron ya gudana mahalartan sun samu damar ziyartar wuraren da aka gudanar da ayyukan a yankunan karkara da matsakaita da manyan biranen da shirin ya samu karbuwa.

 

A lokacin ziyarar sun samu damar tattaunawa da al’ummomin da suka amfana

 

Al’ummomin sun bayyana godiyar su ga gwamnatocin hadi da bankin duniya bisa samar da shirin tare da tabbatar da cigaba da kulawa da ayyukan da akayi masu domin amfani mai dorewa

 

A lokacin da suke taya al’ummomin jihar Katsina murnar cin gajiyar ayyukan na “SURWASH” mahalartan sun kuma jinjinawa gwamnatin jihar bisa nasarar da ta samu wajen aiwatar da shirin, suna masu bayyana jihar a matsayin abun koyi ga sauran jihohin.

 

 

Kamilu Lawal.

Leave A Reply

Your email address will not be published.