Hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama sun kashe mutane da dama a makarantar al-Fakhoora da ke karkashin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza.
Akalla mutane 50 ne suka mutu sakamakon harin bam, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar a ranar Asabar.
“Daruruwan mutane ne ke samun mafaka a cikin wannan makaranta,” in ji wani wakilin Al Jazeera.
Tsarin kiwon lafiya ya ruguje a Gaza, kashi daya ne kawai na matsalar jin kai a cikin fargabar cututtuka da yunwa.
Akalla mutane 12,000 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply