Take a fresh look at your lifestyle.

Dan Majalisa Da NEMA Sun Raba Kayan Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar Ebonyi

0 162

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Ikwo/Ezza ta kudu Kwamared Chinedu Ogah tare da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA sun raba kayan agaji ga wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a karamar hukumar Ikwo dake jihar Ebonyi a kudu maso gabashin Najeriya.

Ogah ya ce rabon kayan agajin a sassan 31 na ‘yan siyasa da kuma rumfunan zabe 497 da ke karamar hukumar, an yi shi ne domin dakile illar da ambaliyar ruwa ta yi wa al’ummar Ebonyi.

“Talakawa su ne karfi na; su ne suka zabe ni. Sun ba ni kwarin gwiwa; shi ya sa duk abin da ya shafe su ya fi damuna.

“Na gode wa shugaban kasa, Bola Tinubu; mataimakin shugaban kasa Shettima; da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Mista Gbajabiamila, domin yin hakan.

“Ina kuma gode wa Gwamnan Jihar Ebonyi Francis Nwifuru saboda yadda ya nuna halin ko-in-kula da kuma kyale Majalisar Dokoki ta kasa da Hukumar NEMA ta amince da hakan.

“Nwifuru mutum ne mai girman zuciya, kuma na yaba masa akan hakan,” in ji Ogah.

Wakilin ofishin shiyyar NEMA na shiyyar Kudu maso Gabas, Mista Nnaynelugo Ezeani, ya yi nuni da bukatar ci gaba da wayar da kan jama’a a cikin al’ummomi daban-daban domin tabbatar da cewa an wayar da kan jama’a yadda ya kamata kan al’amuran da suka shafi gaggawa, ta yadda za a rage illolin da bala’in ke haifarwa.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, wata mata mai nakasa, Misis Nweke Victoria a madadin wasu ta godewa dan majalisar da hukumar NEMA da suka kawo musu dauki.
Ta yi addu’ar Allah ya saka musu da alheri.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *