Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Tsohon Shugaban Sojoji, Manjo Janar Alli

0 70

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajantawa iyalan Alli da sojojin Najeriya bisa rasuwar tsohon babban hafsan sojin kasa, Manjo-Janar Chris Alli (mai ritaya), wanda ya rasu a ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba, 2023.

 

KU KARANTA KUMA: Sojojin Najeriya Sun Yi Zaman Makokin Tsohon Babban Hafsan Sjin Kasa Manjo Janar Chris Alli

 

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya sanyawa hannu, shugaban ya bayyana rasuwar tsohon hafsan sojin a matsayin rashi mai raɗaɗi, inda ya ce ya bauta wa ƙasarsa da aminci.

 

“Ina jajantawa iyalan Alli da sojojin Najeriya kan rashin da aka yi wa tsohon babban hafsan sojin kasa. Ya yi wa kasar shi hidima da daraja kuma ya yi ritaya mai inganci. Allah Madaukakin Sarki Ya jikan shi ya kuma bai wa iyalan sh kwarin guiwar daukar babban rashi,” in ji Shugaban.

 

An haife shi a ranar 25 ga Disamba 1944, a Koton Karfe, Jihar Kogi, marigayi Hafsan Sojan Najeriya ya fara zama a rundunar sojojin Najeriya a ranar 20 ga Oktoba 1967, a matsayin mamba na kwas na gajeren sabis na gaggawa.

 

Marigayi Manjo Janar Alli ya zama Hafsan Soji na tara a watan Nuwamba 1993 har zuwa lokacin da ya yi ritaya daga aiki a watan Agustan 1994.

 

Ya kasance shugaban mulkin soja na jihar Filato Najeriya daga watan Agusta 1985 zuwa 1986 a lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida.

 

Bayan shekaru da yawa, an nada shi shugaban riko na jihar Filato a lokacin rikicin da ya barke a jihar a shekarar 2004 sakamakon kashe-kashen kabilanci a Shendam da ke karamar hukumar Yelwa.

 

Ya kuma yi aiki a matsayin Daraktan leken asiri na soji (DMI), kafin hawansa zuwa babban hafsan soji.

 

Marigayi Manjo Janar Chris Alli ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya a asibitin sojoji dake jihar Legas.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.