Daraktan ma’aikatar lafiya ta Gaza, Mounir el-Boursh ya yi watsi da ikirarin Isra’ila na cewa ta gano wani rami na Hamas a asibitin al-Shifa, yana mai bayyana hakan a matsayin “karya ce karara”.
Akalla mutane takwas ne suka mutu sakamakon harin da Isra’ila ta kai kai tsaye a asibitin arewacin Gaza na Indonesia.
Isra’ila na ci gaba da kai munanan hare-hare a zirin Gaza, inda ta kai hari a wasu yankuna da ke yankin, ciki har da kusa da asibitin Indonesiya.
Sama da mutane 13,000 ne aka kashe a yanzu tun lokacin da aka fara kai harin a ranar 7 ga watan Oktoba.
Kwamitin kare hakkin ‘yan jarida ya ce an kashe ‘yan jarida 48 da ma’aikatan yada labarai tun farkon rikicin; 43 daga cikin wadanda aka kashen Falasdinawa ne, hudu kuma ‘yan Isra’ila ne, daya kuma dan kasar Lebanon ne.
‘Yan tawayen Houthi na Yaman sun kwace wani jirgin ruwan dakon kaya da ke da alaka da Isra’ila a cikin tekun Bahar Rum tare da yin garkuwa da ma’aikatansa guda biyu, lamarin da ya kara dagula fargabar barkewar rikici.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce ta kwashe jarirai 31 da ba su kai ga haihuwa ba daga asibitin al-Shifa zuwa asibitocin Turai da Nasser da ke kudancin Gaza. Sama da marasa lafiya 200 har yanzu suna makale a asibiti.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply