Isra’ila da Hamas sun amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta na wucin gadi da za ta ba da damar sakin mutane kusan 50 da ake tsare da su a Gaza tun bayan da kungiyar Hamas ta mamaye kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, a madadin Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yari na Isra’ila.
Majalisar zartaswar Isra’ila ta goyi bayan yarjejeniyar bayan tattaunawa kan yarjejeniyar da Qatar ta shiga tsakaninta da ta ci gaba da faruwa da sanyin safiyar Laraba, inda kafafen yada labarai na Isra’ila suka rawaito cewa an yi ta musayar kalamai masu zafi tsakanin ministocin gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu.
A karshe mambobi uku ne kawai daga cikin 38 na majalisar ministocin kasar suka kada kuri’ar kin amincewa da sulhun – Ministan Tsaron kasar Itamar Ben-Gvir da wasu ‘yan jam’iyyarsa masu ra’ayin rikau.
Ofishin firaministan kasar ya ce yarjejeniyar za ta bukaci Hamas ta sako mata da yara akalla 50 a zaman sulhu na kwanaki hudu. Ya ce, ga duk wasu karin mutane 10 da aka yi garkuwa da su, za a tsawaita zaman da rana guda, ba tare da ambaton sakin fursunonin Falasdinu ba a musaya.
“Gwamnatin Isra’ila ta kuduri aniyar mayar da dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su gida. A daren yau, ta amince da shirin a matsayin matakin farko na cimma wannan buri,” in ji ta a takaice.
Kungiyar Hamas da ke iko da Gaza ita ma ta fitar da wata sanarwa, inda ta tabbatar da cewa za a kubutar da mata da kananan yara 50 da ake tsare da su a yankin, a maimakon Isra’ila ta sako mata da kananan yara Palasdinawa 150 daga gidajen yari na Isra’ila.
Ya ce Isra’ila za ta kuma dakatar da duk wani matakin soji a Gaza kuma za a bar daruruwan manyan motocin da ke dauke da kayan agaji, da magunguna da kuma man fetur zuwa cikin yankin.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply