Kungiyar Hamas ta bayyana cewa kimanin mutane 30 ne suka mutu a harin da Isra’ila ta kai kan wata makarantar da ke da alaka da Majalisar Dinkin Duniya a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke Arewacin Gaza, a daidai lokacin da lokaci ya kure da shirin sasantawa tsakanin kungiyar Falasdinu da Isra’ila.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ba da rahoton mutuwar mutane 27 daga wannan harin da aka kai a makarantar Abu Hussein da ke karkashin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), wanda ke dauke da Falasdinawa da suka rasa matsugunansu da ke tserewa tashin hankali da kuma mummunar tashin bamabamai a wasu sassan Gaza.
Sojojin Isra’ila sun kuma kaddamar da sabbin hare-hare a asibitin Indonesiya da ke arewacin Gaza, inda suka nufi babbar kofar shiga da injinan wutar lantarki.
Ashraf al-Qudra, kakakin ma’aikatar, ya ce asibitin ya shiga cikin “mummunan harin bama-bamai”, kuma ana kai hari kan “bangaren ginin”.
Sama da majiyyata 200, da ma’aikatan lafiya, da kuma ‘yan gudun hijira na cikin gida a halin yanzu suna asibiti a Beit Lahiya, wanda aka yi wa kawanya tsawon mako guda.
A gefe guda kuma jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hari a unguwar Sheikh Nasser da ke Khan Younis a kudancin zirin Gaza, inda suka kashe akalla mutane biyar tare da jikkata wasu da dama, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu, Wafa.
An kuma bayar da rahoton cewa akalla mutane 10 ne suka mutu a lokacin da sojojin Isra’ila suka kai hari a wani gida da ke unguwar Sheikh Radwan a arewacin Gaza.
A yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye, an harbe Mohammed Ibrahim Fuad Edely dan shekaru 12 da haihuwa, a cewar ma’aikatar Falasdinawa da sojojin Isra’ila suka yi.
Lamarin dai ya kawo adadin Falasdinawa da aka kashe a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye tun ranar 7 ga watan Oktoba zuwa 229, 52 daga cikinsu yara ne.
Hare-haren bama-bamai da Isra’ila ta kai ya kashe mutane fiye da 14,800 a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar jami’an Falasdinawa.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply