A ranar Juma’a ne mai shiga tsakani na Qatar ya ce za a fara tsagaita wuta na kwanaki hudu da Isra’ila da Hamas suka amince.
Mafarin tsagaita bude wuta na kwanaki hudu a ranar Juma’a, zai zama na farko da aka dakatar a yakin kusan makonni bakwai.
Yarjejeniyar da Qatar ta sanar ta kunshi tsagaita wuta na kwanaki hudu a fada tsakanin bangarorin biyu domin barin agajin da ake bukata a Gaza.
Zirin Gaza na jurewa dare da munanan hare-haren bama-bamai daga “iska, kasa, da ruwa” gabanin fara sasantawa tsakanin Qatar, in ji MDD.
Wata ‘yar jaridar Falasdinu, Amal Zuhd, da ‘yan uwa da aka kashe a birnin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Wafa.
Sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare cikin dare a yammacin gabar kogin Jordan da suka mamaye inda aka kashe Falasdinawa 211 tun fara yakin.
Fiye da mutane 14,800 aka kashe a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.
Leave a Reply