Majalisar Dattawan Najeriya ta umurci kwaminta mai kula da harkokin sharia, da yancin dan Adam da kuma harkokin sharia da ya gaggauta ganawa da ofishin babban mai sharia na tarayya domin fara aikin sake duba dokokin tarayyar Najeriya na shekarar 2004.
Bukatar hakan na kunshe a cikin wani kudiri da sanata Shehu Kaka Lawal daga Jihar Borno ya gabatar a zaman majalisar na ranar talata.
Da yake jagorantar muhawarar Sanata Shehu ya ce, Dokokin Tarayyar Najeriya, wasu jerin alkaluma ne na dokokin kasa da ake aiki da su a Najeriya wadanda ake sabunta su akai-akai.
Ya ce ana tattara dokokin kasa ne a karkashin ikon ministan sharia na kasa, muddin majalisar dokokin kasar ta amince da wata doka.
Sanata Shehu, ya ce an jima ba a tattara dokokin kasa wuri guda ba tun a shekarar 2004, kuma gaggauta yin hakan yanzu ba tare da bata lokaci ba zai kasance mai mutukar anfani ga tsarin mulkin dimokaradiyya a Najeriya.
Har ila yau sanatan ya bukaci yin garanbawul ga dokokin kasa da suka shafe kusan shekaru ashirin da suka gabata.
Ya ce gyaran dokokin yana da mutukar mahinmanci domin zai tamakawa lauyoyi da alkalan da suke hukunci da dalibai da ma malaman jamioi domin saukaka ayyyukansu.
“Akwai dokoki goma sha shida da muke so a yi wa garanbawul kana a sanya yasu a yanar gizo ta yadda duk mai bukatarsu zai danna ya shiga inda suke daga in da yake, yin hakan zai taimaka wajen saukaka ayyukan jamaa, saboda haka irin wannan amfanin muke so.” In ji Sanata Kaka
Daga karshe bayan tafka mahawa majalisar Dattawa ta goyi bayan bukatun da aka gabatar a cikin kudirin inda shugaban Majalisar Sanata Godswill Akpabio ya umarci kwamitin majalisar mai kula da harkokin sharia da ya gaggauta aiwatar da matakin da aka dauka kana ya gabatar mata da rohoto.
Abdulkarim Rabiu
Leave a Reply