Take a fresh look at your lifestyle.

Taron kolin Sin Da Gabas Ta Tsakiya: ‘Isra’ila Na Neman Kawo Karshen Falasdinawa’

0 33

Ministan harkokin wajen Falasdinu ya ce Isra’ila na neman kawo karshen kasancewar al’ummar Falasdinu a “kasa mai tarihi.”

 

Kalaman na Riyad al-Maliki sun zo ne a daidai lokacin da jami’an diflomasiyya daga kasashen Larabawa da musulmi suka gana da takwarorinsu na kasar Sin a birnin Beijing a ranar Litinin.

 

Beijing na karbar bakuncin tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Falasdinu, Indonesia, Masar, Saudiyya da kuma Jordan domin tattaunawa da nufin samar da mafita don kawo karshen yakin zirin Gaza.

 

Taron, wanda a lokacin da kasar Sin ta yi alkawarin yin aiki don “dawo da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya”, ana kallon shi a matsayin wani yunkuri na Beijing na kara taka rawar da take takawa a duniya.

 

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, al-Maliki na hukumar Falasdinu ya zargi Isra’ila da neman “kawo karshen zaman al’ummar Falasdinu a kan abin da ya rage na kasarta mai tarihi.”

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Masar ya ce korar Falasdinawa daga zirin Gaza zai yi barazana ga zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a yankin da ma duniya baki daya.

 

“Masar na yin iyakacin kokarinta na shigar da kayan agaji a zirin Gaza ta mashigar Rafah, amma manufar Isra’ila na dakile shigar da kayan agaji wata manufa ce ta tsattsauran ra’ayi da nufin tura Falasdinawa ficewa daga yankin karkashin nauyin harin bama-bamai.” Kakakin ya ce.

 

Kasar Sin wadda ita ce mai masaukin baki, ta kasance a tarihi tana tausayawa Falasdinawa. Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya shaidawa jami’an diflomasiyyar da suka ziyarci kasar cewa, kasarsa na iya ganin cewa ” bala’in jin kai na faruwa a Gaza” kuma dole ne a dakatar da shi.

 

“Halin da ake ciki a Gaza ya shafi dukkanin kasashe a duniya, suna yin tambaya game da tunanin dan Adam na gaskiya da kuskure da kuma layin ‘yan adam,” in ji shi, kafin ya bukaci kasashen duniya da su “yi gaggawar gaggawa” don hana yaduwar yakin.

 

Bayan barkewar yakin a watan da ya gabata, Wang ya shaida wa takwaransa na Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud a wata wayar tarho cewa “Ayyukan Isra’ila sun wuce kare kansu”.

 

Wang da sauran jami’an kasar Sin sun yi kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa tare da “kwantar da hankali” halin da ake ciki.

 

 

 

ALJAZEERA/Ladan Nasidi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.