Ostiraliya Ta Yi Maraba Da Tsagaita Wuta Tsakanin Isra’ila Da Hamas
Firayim Ministan Australiya, Anthony Albanese ya ce tsagaita wuta a yakin Isra’ila da Hamas ya nuna “muhimmiyar ci gaba” a rikicin, yayin da ya yi maraba da sakin mutanen da kungiyar Islama ta Falasdinawa ta Hamas ta yi.
Rahoton ya ce mayakan Hamas sun sako mutane 24 da aka yi garkuwa da su a ranar Juma’a a rana ta farko na tsagaita bude wuta na farko bayan da bindigogi suka yi shiru a zirin Gaza a karon farko cikin makonni bakwai.
“Ostiraliya na maraba da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma dakatar da tashin hankali don ba da damar samun damar shiga Gaza,” in ji Albanese a dandalin sada zumunta na X.
“Abubuwan da ke faruwa a yau suna wakiltar ci gaba mai mahimmanci kuma Ostiraliya na maraba da su.”
A halin da ake ciki, gwamnatin Ostireliya a baya ta bukaci a dakatar da tashin hankali, kuma ta yi kakkausar suka ga Hamas, yayin da ta yi kira ga Isra’ila da ta yi taka-tsan-tsan don rage asarar fararen hula.
“Mun ci gaba da yin kira da a saki duk wadanda aka yi garkuwa da su, don kare rayukan fararen hula da kuma daukar matakai na tsagaita bude wuta da kuma zaman lafiya mai dorewa,” in ji Albanese a kan X.
A Ostiraliya, rikicin ya janyo zanga-zanga daga kungiyoyin Yahudawa da Falasdinawa, inda dubbai suka fito domin gudanar da gangami a manyan biranen kasar.
REUTERS/Ladan Nasidi.
Leave a Reply