Sama da Falasdinawa 20 ne aka kashe tun bayan da sojojin Isra’ila suka sake kai hare-hare a Gaza bayan wa’adin tsagaita bude wuta, in ji jami’an lafiya.
Dakatarwar ta kwanaki bakwai da ta fara a ranar 24 ga watan Nuwamba kuma aka tsawaita sau biyu, ta bada damar yin musayar fursunonin Falasdinawan da dama da aka yi garkuwa da su a Gaza da kuma saukaka shigar da kayan agajin jin kai a gabar tekun da ta lalace.
“Tare da sake barkewar fada muna jaddada cewa: Gwamnatin Isra’ila ta kuduri aniyar cimma manufofin yakin don kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da mu, don kawar da Hamas, da kuma tabbatar da cewa Gaza ba za ta taba yin barazana ga mazauna Isra’ila ba.” Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce a cikin wata sanarwa.
“Abin da Isra’ila ba ta cimma ba a cikin kwanaki hamsin kafin tsagaita bude wuta, ba za ta cimma ba ta hanyar ci gaba da kai hare-hare bayan tsagaita bude wuta,” in ji Ezzat El Rashq, mamba a ofishin siyasa na Hamas a shafin yanar gizon kungiyar.
Kafofin yada labaran Falasdinu da ma’aikatar harkokin cikin gida ta Gaza sun ba da rahoton cewa Isra’ila ta kai hare-hare ta sama da kuma manyan bindigogi a fadin yankin bayan wa’adin tsagaita bude wuta, ciki har da Rafah, kusa da kan iyaka da Masar.
A Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, wani shaida na kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce yana jin karar harbe-harbe da kuma ganin hayaki na tashi a gabashin garin. Ya kara da cewa mutane na ta tserewa daga yankin zuwa sansanonin da ke yammacin Khan Younis domin fakewa.
Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, an kashe mutane da dama da jikkata sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai musu.
Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa jiragenta na kai farmaki kan mayakan Hamas a Gaza.
Hotunan da aka yi a shafukan sada zumunta sun nuna hayaki mai tarin yawa na tashi a kan sansanin Jabalia da aka gina a Gaza.
Bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, Isra’ila ta mayar da martani da mummunan harin bama-bamai da kuma mamayar kasa a Gaza.
Hukumomin lafiya na Falasdinu da Majalisar Dinkin Duniya ke ganin abin dogara sun ce an tabbatar da kashe mutanen Gaza fiye da 15,000.
REUTERS/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply