Take a fresh look at your lifestyle.

‘Dan Adawar Uganda Ya Ziyarci Burtaniya Bayan Zargin Hana Shi Visa

0 106

Shahararren dan majalisar adawar Uganda kuma tsohon fitaccen mawaki, Bobi Wine, ya yi wani gagarumin ci gaba tare da ziyarar shi ta farko a Burtaniya bayan shekaru goma.

 

Wannan na zuwa ne makonni uku kacal bayan matakin da gwamnatin Burtaniya ta dauka na dage takunkumin hana shiga kasar na tsawon shekaru tara da aka yi masa.

 

Da yake raba sha’awar sa, Bobi Wine ya dauki hotonsa a dandalin sada zumunta, inda ya sanya hotonsa a wajen babban ofishin BBC na London tare da taken, “London, shekara 10 ke nan!” Ana zargin haramcin shigar Bobi Wine zuwa Burtaniya da wakarsa mai suna “Burn Dem” a shekarar 2014, inda kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka yi suka kan zargin tallata hare-haren ‘yan luwadi.

 

A kololuwar aikin shi, an hana Bobi Wine bizar Burtaniya jim kadan bayan fitar da wakar, lamarin da ya tilasta mashi soke wasanni biyu da aka shirya yi a kasar.

 

A lokacin, Ofishin Cikin Gida na Burtaniya ya ki tabbatar da ko ya hana shigar Bobi Wine lokacin da manema labarai suka tuntube shi.

 

A ranar 5 ga Nuwamba, Bobi Wine, ainihin suna Robert Kyagulanyi, ya ce a ƙarshe ya sami damar komawa Burtaniya.

 

“Na yi matukar farin cikin sanar da ku cewa an soke haramcin da aka yi mini na shiga Burtaniya, kuma nan ba da jimawa ba zan ziyarci Burtaniya bayan fiye da shekaru 10,” in ji Bobi Wine a kan X.

 

Ya kara da cewa tawagar lauyoyin sa sun yi jajircewa wajen ganin an dage dokar hana zirga-zirga.

 

 

 

Africanews/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *