Take a fresh look at your lifestyle.

Kamfanin Oppenheimer Na S’Afrika Ya Sayi Hannun Jari Kashi 100% Na kamfanin Abin Sha

0 89

Dan, Nicky Oppenheimer Hamshakin attajirin nan na Afirka ta Kudu Jonathan Oppenheimer,ya mallaki kaso mafi tsoka a babban kamfanin sarrafa abin sha a Najeriya, GZ Industries.

 

Rahotanni sun ce yarjejeniyar da aka sanar a cikin wata sanarwa daga Afirma Capital, wanda aka fi sani da Standard Chartered Private Equity, ba ta bada bayanan kudi ba.

 

Oppenheimer ya sayi hannun jarin Afirma Capital na kashi 37.5 na GZI, wanda ke samar da gwangwani ga kamfanoni da suka hada da Coca-Cola Co. Kafin wannan sabon saye, Oppenheimer ya riga ya mallaki kashi 62.5 cikin 100 na hannun jarin GZI.

 

Oppenheimer ya fara siyan kasuwancin ne a cikin 2018, lokacin da GZI ya gina masana’anta a Afirka ta Kudu kuma Afirma ya fara saka hannun jari a GZI a cikin 2012.

 

Wannan ciniki dai na nuni da cewa an samu ci gaba a tattalin arzikin Najeriya musamman yadda shugaban kasa Bola Tinubu da ‘yan majalisar ministocinsa ke ta kokarin kara zuba jari a Najeriya.

 

Rahotanni sun ce, sayen zai baiwa Oppenheimer damar sanin makomar GZI a Najeriya da yankin yammacin Afirka.

 

GZI na samar da gwangwani biliyan uku a kowace shekara a Afirka.

 

Rahotanni sun ce Afirma Capital ya zuba jari a kamfanoni 11 a Afirka tun daga shekarar 2008, kuma ya kammala ficewa daga takwas, inda ya mayar da sama da dala miliyan 800 ga masu zuba jari a tsawon lokacin.

 

 

 

Punch/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *