Take a fresh look at your lifestyle.

‘Yan Sanda Sun Damke ‘Yan Damfara Biyu A Jahar Neja

Nura Mohammed, Niger.

0 378

Rudunar Yan sandan Najeriya reshin Jahar Neja dake arewa ta tsakiyar kasar ta kama wasu mutane biyu da ake zargin su da damfarar al’umma ta hanyar karbar kudaden rejista don yin karatu a makaratar kiwon lafiya ta boge da aka buda a yankin Mai Kunkele dake karamar hukumar Bosso.

Rudunar ‘yan sandan ta bayyana hakan ne a takarar da ta rabawa manema labarai dake dauke da sa hannu kakakin rudunar a Jahar Neja DSP Wasiu Abiodun.

Rudunar ta Kara da cewar bayan samun sahihan bayanan sirri jami’an ta sun kai samame inda suka yi nasarar kame Daniel Ishaya mai shekaru 23 dan asalin garin Gurmama na karamar hukumar Shiroro a jahar ta Neja da ya bude makaratar, sai Francis Ede Mai shekaru 30 dan asalin jahar Enugu a kudu maso gabashin Najeriya dake zama Darakta a kwalejin ta Excellence College of Health Science and Technology.

Hakazalika, rudunar ta ce bayan gudanar da binciken farko ta gano cewar Daniel Ishaya ya yiwa dalibai Dari rijista inda kowannan su ya biya naira dubu saba’in da takwas (78,000) a matsayin kudin makarata tare da taimakon Daraktansa Francis Ede da sauran ma’aikatan da ya dauka su ashirin malamai dake koyarwa a makaratar.

 

Takardar ta Kuma bayyana cewar Kwamishinan ‘Yan sandan jahar Monday Bala Kuryas ya bukaci al’umma da su gudanar da bincike don tabbatar da sahihancin makarantu kafin sanya kudaden su domin kaucewa shiga hannu Yan damfara.

Rudunar ta Kuma ce da zarar ta Kammala bincike zata gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuto domin fuskantar shari’a.

Nura Mohammed.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *