Take a fresh look at your lifestyle.

Kaduna: Wutar Daji Ce Ta Hadasa Gobarar FRCN

3 178

Hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna ta ce kona daji ne ya haddasa gobarar da ta tashi a gidan rediyon tarayyar Najeriya FRCN a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya.

 

Mataimakin kwamandan hukumar, Ayuba Yohanna, ya tabbatar da hakan a ranar Lahadin da ta gabata a wata tattaunawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, a Kaduna.

 

A cewarsa, “Gobarar ta tashi ne daga daji da ke bayan ofishin .”

 

 

Ya ce jami’an da ke bakin aiki sun garzaya wurin da lamarin ya faru bayan sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 1:45 na rana.

 

Yohanna ya ce “Ofisoshi biyu na sashen sayan kayayyaki abun bai shafa ba tare da asarar rayuka ko jikkata ba.”

 

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Malagi, ya yi alkawarin gudanar da gyare-gyare a gidajen rediyo da kuma NTA.

 

 

 

NAN/Ladan Nasidi.

3 responses to “Kaduna: Wutar Daji Ce Ta Hadasa Gobarar FRCN”

  1. I was more than happy to find this page. I wanted to thank you for ones
    time just for this wonderful read!! I definitely savored every bit of it and i also have you saved as a favorite to check out new information on your blog.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *