Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayar da gudummawar Naira miliyan 200 ga iyalan wadanda harin da jirgin yaki mara matuki ya rutsa da su a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Shugaban wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara, Malam AbdulRahman AbdulRazaq ya yi hakan a madadin taron a lokacin ziyarar jaje da ya kai jihar Kaduna.
Yayin ganawarsa da gwamnan jihar Uba Sani, Abdulrazaq ya mika sakon ta’aziyyar taron ga gwamnatin jihar da iyalan wadanda suka rasu da kuma mutanen jihar.
AbdulRazaq ya bayyana kwarin gwuiwarsa kan binciken da aka yi a kan lamarin inda ya ce hakan zai taimaka wajen dakile irin wannan bala’in da ba a yi niyya ba a nan gaba.
Sai dai ya yabawa Gwamna Sani, da hukumomin soji da kuma shugabannin al’ummar Kaduna inda ya ce “Ina yaba wa Gwamna Uba Sani, da hukumomin soji, da shugabannin al’ummar Kaduna bisa yadda suke nuna halin jaha da balaga da suka gudanar da ayyukan da ba a yi niyya ba.”
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Lahadi 3 ga watan Disamba, 2023, sojojin Najeriya sun kai wani hari da jiragen yaki mara matuki a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna inda suka yi wa wasu gungun ‘yan fashi da makami hari amma sojojin sun yi kuskure a wani kauye, ya kashe fararen hula sama da 100.