Samar da tallafi a bangaren ilimi mai zurfi na daga cikin al’amurran da ke gasa wa iyaye da dalibai su kansu aya a hannu duba da yadda rayuwa ke kara tsada. A bisa haka ne ake kara yin kira ga masu hannu da shuni da yan siyasa da su duba wannan lamarin da idon basira inda tuni wasu suka fara amsa kira.
Sanata Ibrahim Lamido da ke wakiltar yankin Sokoto ta gabas arewa maso yammacin Najeriya na cikin wadanda suka amsa wannan kiran, inda ya bayar da tallafin kuɗi ga dalibai dubu daya daga yankin nasa. Ɗaliban sun amfana da tsabar kuɗi wuri na gugar wuri har naira dubu hamsi (50,000) ga ko wane ɗalibi.
Gabashin yankin na Sokoto, yanki ne da ke fama da tashe-tashen hankullan masu sata da garkuwa da mutane inda ɗunbin al’umma ke cike da bukatar tallafi da ya haɗa da na ilimi wanda hakan ne a cewar Alhaji Muhammadu Sarkin Alaru da ya wakilci Sanatan zai taimaka wajen ɗorewar karatun yaran.
“Wannan tallafin da mai girma Sanata Ibrahim Lamido ya bayar ga ɗalibai zai taimaka wajen ci gaban karatunsu kuma yana daga cikin abinda muka alƙawullanta yayin yaƙin neman zaɓe.” in ji Sarkin Alaru
Ɗaliban da suka amfana da tallafin kuɗin sun yi fatan Allah san barka.
Kwamared Daniyalu Bello Mailafiya da ke zama shugaban ɗaliban yankin ya ce ba ga tallafin kuɗi Sanatan ya tsaya ba har da samar da guraben karatu.
“Kimanin matasa da dama ne suka samu guraben karatu tare da ɗaukar nauyinsu, a jami’ar Usmanu Danfodiyo kuwa duk ɗalibin da ya fito daga yankin an sauke masa kashi hamsin cikin ɗari na kuɗin makaranta “
A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Sokoto arewa maso yammacin Najeriya ta yi alƙawalin ci gaba da haɗa hannu da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi wajen samawa ɗalibai tallafi.
Abdulkarim Rabiu