Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Jam’iyyar SDP Ya Daukaka Martabar Marigayi Akeredolu Da Na’abba

143

Shugaban jam’iyyar Social Democratic Party, SDP na kasa, Mista Shehu Gabam ya bayyana rasuwar tsohon kakakin majalisar dokoki ta kasa Dr Ghali Na’abba da kuma marigayi gwamnan jihar Ondo Mista Rotimi Akeredolu a matsayin babban rashi ga kasar nan.

 

A cikin sakon ta’aziyyar, Gabam wanda ya bayyana irin gudunmawar da suke bayarwa ga al’ummar kasar ya bayyana cewa Ghali Na’abba ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban dimokradiyya a Najeriya.

 

Gabam ya yi kira ga al’ummar jihohin Ondo da Kano da ma al’ummar kasar baki daya da su hada kai wajen yin addu’a tare da alhinin rashin wadannan fitattun shugabanni.

 

Ya bayyana cewa rasuwar fitattun mutane biyu babban rashi ne ga Najeriya domin sun kasance shugabanni na kwarai, kuma abin da suka gada zai dawwama a cikin zukata da tunanin mutanen da suka yi wa hidima.

 

Mista Gabam ya kara mika tunani da addu’o’in jam’iyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu yayin da yake addu’ar Allah ya jikan su.

 

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.