Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Nurar amani a Najeriya, Farfesa Isa Pantami ya amince da nadin Mista Bulus Yakubu a matsayin mukaddashin babban jami’in Gidan waya na Najeriya, NIPOST, bayan dakatar da Dakta Ismail Adebayo Adewusi daga mukaminsa.
Mista Yakubu wanda ya yi digirin farko a fannin shari’a daga Jami’ar Ahmadu Bello, ya shiga aikin ma’aikatan gidan waya a shekarar 1990.
Yakubu dan asalin garin Takum ne da ke karamar hukumar Takum a jihar Taraba.
Har zuwa lokacin nadin nasa, ya kasance sakataren hukumar gudanarwar NIPOST, daraktan ayyuka na musamman da kuma jami’in hulda da jama’a na NIPOST a majalisar dokokin kasar.
A matsayinsa na gogaggen Jami’in Jama’a, ya kuma yi aiki a matsayin Sakatare da Mai Bada Shawara Kan Shari’a na NIPOST 2007 zuwa 2017 tare da tabbataccen sanin kyakkyawan aiki.
Ya kasance mamba na ƙwararrun ƙungiyoyin musamman, Ƙungiyar lauyoyi ta Duniya (IBA), Ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) kuma shi ne shugaban kwamitin kwararrun shari’a na Pan African Postal Union (PAPU).
Mista Yakubu ma’aikaci ne a Cibiyar Gudanar da Harkokin Kasuwanci ta Najeriya.
Leave a Reply