Girgizar kasa mai karfin awo 7.6 ta afku a tsakiyar kasar Japan ranar Litinin, wanda ya haifar da gargadin tsunami da kuma shawarwari ga mazauna yankin da su kaura.
Tsunami mai tsayin mita 1 ta afku a sassan gabar tekun da ke gabar tekun Japan inda ake sa ran zazzafar igiyar ruwa mai karfi, kamar yadda kafar yada labarai ta NHK ta ruwaito.
Hukumar Kula da Yanayi ta Japan ta yi gargadin afkuwar Tsunami ga lardunan Ishikawa, Niigata da Toyama da ke gabar teku.
Wutar Lantarki ta Hokuriku (9505.T)
NHK ta ce tana binciken duk wata matsala a tashoshin nukiliyarta.
Mai magana da yawun kamfanin Kansai Electric Power (9503.T) ya ce a halin yanzu babu wata matsala a tashoshin ta na nukiliya amma kamfanin na sa ido sosai kan lamarin.
Wata babbar girgizar kasa da tsunami ta afku a arewa maso gabashin Japan a ranar 11 ga Maris, 2011,da kuma barna a garuruwa da haddasa narkewar nukiliya a Fukushima.
REUTERS/Ladan Nasidi.