Take a fresh look at your lifestyle.

NAJERIYA TA DAGE HARAMCIN ANFANI DA SHAFIN SADA ZUMU NTA NA Twitter

0 326

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dage haramcin anfani da shafin sada zumunta na daga ranar 13 ga watan Janairu shekara ta 2022.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga shugaban kwamitin kula da harkokin shafin sada zumunta na Najeriya da Twitter, Kashifu Inuwa wanda kuma darakta janar ne a hukumar yada labarun sadarwa ta Najeriya, NITDA.
“Gwamnatin tarayya (FGN) ta umurce ni in sheida wa alumma cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da dage haramcin ko kuma takunkumin da ya hana anfani da shafin Twitter a Najeriya daga daren 13th January 2022.
“Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da Ministan Sadarwa da tattalin arzikin Naura mai yatsu, Farfesa Isa Pantami .
“Idan baku manta ba a ranar 5th Yuni 2021, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bakin Ministan yada labaru da aladu Alh Lai Mohammed. Ya bada sanarwar haramta anfani da shafin sada zumunta na Twitter
“Wannan na daga cikin abunda yake ciwa kasa tuwo a kwarya musamman harkar tsaro,shi ya sanyaFGN ta dakatar da anfani da shafin na Twitter a Najeriya.
“Hanyoyin da aka bi wajen sulhu tsakanin Gwamnatin Najeriya da kanfanin Twitter Inc. ya taimaka fahimtar ci gaba nan gaba.

Ladan Nasidi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *