Take a fresh look at your lifestyle.

Mutun 1,435 Suka Anfana Da Tallafin Shugaban kungiyar CAN A Jihar Neja

Nura Muhammed ,Minna.

141

Shugaban kungiyar Kristoci ta kasa CAN  reshen jihar Neja, kana babban limamin cucin Catholic na Kontagora dake jihar Neja arewa ta tsakiyar Najeriya  Most Rev Bulus Dauwa Yohanna ya raba kudi da Kayayyakin abinci ga mutane 1,435 a jihohin Neja da Kebbi.

 

Babban limamin ya raba kudi da taliyar indomie da Kayayyakin dandanon girki da lemon na ruwa da buhuhunan shinkafa da masara ga mabiya addin kirstan dake ibadar su a cucin Catholic na Kontagoran.

 

Da yake yiwa manema labarai jawabi Shugaban kungiyar Kristocin na jihar Neja, Bishop Yohanna ya ce wannan karamcin na tallafawa alumma da aka saba yi duk shekara zai taimakawa matan  da mazajen su suka mutu suka bar masu yara kanana.

 

Ya kara da cewar, “Hakan wani mataki ne na kawo saukin rayuwa ga alumma musamman mata da aka bae masu yara, da Kuma wadanda ke cikin halin kuncin rayuwa a cikin alumma “

 

Bishop Yohanna Dauwa ya ce  ana samun Karin alummar dake shiga halin damuwa sakamakon matsi na tattalin arziki dake ake fama da shi a kasar baki daya.

 

“An sami karin alummar dake ke anfana da tallafin, bisa yadda a baya aka baiwa mutun 1000 , Amma a wannan shekarar an sami Karin mutun sama da Dari hudu da suka anfana da tallafin a jihohin Neja da Kebbi.” Bishop Yohanna

 

Wasu daga cikin wadanda suka anfana da tallafin sun nuna Jin dadin su bisa karamcin da aka nuna masu na Basu Kayayyakin abinci da Kuma kudi da zai taimakawa rayuwar su.

 

Hakazalika sun Kuma yabawa babban limamin bisa irin yadda ya himmatu wajan ganin ya taba rayuwar alumma ta hanyar kawo masu sauki da Kuma kulla da halin da suke ciki.

 

Malam Asabe wace take cikin wadanda suka anfana da tallafin ta bayana cewar hakan zai kawo sauki ga alumma da Kuma Kara Basu kwarin gwiwar cigaba da ayyukan Ibadan su.

 

 

Nura Muhammed.

Comments are closed.