Rundunar ‘yan sandan Najeriya dake jihar Katsina arewa maso yamma ta kama mutane 1,627 wadanda ake zargi da laifuka daban daban a shekarar 2023 data gabata
Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Aliyu Abubakar shine ya bayyana hakan lokacin da yake wa manema labarai jawabi dangane da nasarorin da rundunar ta samu cikin shekarar 2023 data gabata
CP Aliyu Abubakar ya bayyana cewa daga cikin wadanda rundunar ta samu nasarar kamawa akwai mutane 258 da ake zargi da fashi da makami da kuma wasu mutane 64 da ake zargi da garkuwa da mutane
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa duk a cikin shekarar ta 2023 rundunar tayi nasarar kama mutane 176 da ake zargi da kisan kai da mutane 69 da ake zargi da cin zarafin yara.
“Akwai kuma sauran mutane 495 da ake zargi da nau’ikan laifuka daban daban”, in jishi.
CP Aliyu Abubakar yace daga cikin jimillar wadanda ake zargi an mika 855 zuwa kotuna daban daban domin fuskantar laifukan da suka aikata.
Ya kara da cewa a bangaren yaki da masu garkuwa da mutane, rundunar tayi nasarar kubutar da mutane 171 daga hannun masu garkuwa da mutanen a maboyar ‘yan bindiga daban daban, hadi da mutane 67 da aka samu nasarar kubutarwa daga hannun masu safarar bil’adama
CP Abubakar wanda ya bayyana cewa a cikin shekarar ta 2023 data gabata, rundunar tayi nasarar kwato muggan makamai da daruruwan dabbobi da babura hadi da wayoyin hannu daga hannun masu laifuka, ta kuma samu nasarar hallaka ‘yan bindiga 17 a kokarin kubutar da mutanen da akayi garkuwa dasu a lokuta daban daban
” Mun ceto mutane 171 da akayi garkuwa dasu da mutane 67 daga hannun masu safarar bil’adama.
“Mun kuma samu nasarar kwato bindiga kirar AK 47 guda 12 da sama da harsashe 1500 hadi da dabbobi 700 da babura da wayoyin hannu”_ inji kwamishinan.
Ya godema babban sufeton ‘yan sandan Najeriya da gwamnatin jihar Katsina da al’ummar jihar Katsina bisa gudummuwar su wajen samun gagarumar nasara akan masu laifuka a cikin shekarar
Kazalika ya bukaci ci gaba da samun hadin kai daga al’ummar jihar domin kawo karshen ta’addanci da sauran laifuka a cikin jihar ta Katsina da Najeriya baki daya.
Kamilu Lawal.