Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Mali Ta Yi Bikin Cika Shekaru 62 Da Samun ‘Yancin Kai

0 40

Kasar Mali da ke yammacin Afirka ta yi bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai.

Shugaban kasar Kanar Assimi Goita, wanda ke rike da madafun iko tun bayan juyin mulkin shekaru biyu da suka gabata, ya yi bitar sojoji a wani faretin soji na bikin a Bamako babban birnin kasar.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Guinea, Kanar Mamady Doumbouya ne ya tare shi a faretin.

Kasar Mali dai ta fuskanci warewar kasashen duniya tun bayan da sojoji suka kwace mulki.

Ya zuwa yanzu Kanar Goita ya gaza cika wa’adin kasa da kasa na shirya sabon zabe na dimokuradiyya da kuma tsare sojojin Ivory Coast 46 ya haifar da tashin hankali da makwabciyar kudanci Mali.

A watan Yuni, hukumomin Mali sun ce “ba za su ba wa tawagar Majalisar Dinkin Duniya izinin gudanar da bincike kan take hakkin bil’adama a Mali ba, ciki har da mutuwar fararen hula fiye da 300 a farkon wannan shekarar.”

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun zargi sojojin Mali da aikata kisan.

Kasar Faransa wacce ta taba yin mulkin mallaka a karo na farko da ta kwashe shekaru tara tana yaki da tsattsauran ra’ayin Islama a kasar Mali, ta kammala janyewar sojojinta daga kasar a watan da ya gabata.

labaran africa

Leave A Reply

Your email address will not be published.